Majalisar limamai da malamai ta Jihar Kaduna ta bayyana shirinta na tattaunawa da yan takarar gwamna a jihar don ba al’ummar musulmi damar fahimtar shirye-shirye da kowannensu ke da shi, na ciyar da jihar gaba.
Mataimakin sakataren kwamitin, Imam Musa Tanimu, yayin jawabin da ya yi wurin taron manema labarai a ranar Laraba, ya ce dalilin taron shine nusantar da mambobinta kan bukatar zaben shugabanni masu gaskiya da rikon amana da za su mulki jihar.
Amma ya fayyace cewa majalisar ba da ta wani dan takara da ta take goyon baya, ya kara da cewa: “Mun shirya taron tattaunawar ne don mambobinmu su fahimci inda dukkan yan takarar suka dosa, su kuma yanke shawara mai kyau.”
A cewarsa, tun da farko kwamitin ta janyo hankulan yan siyasa su guji furta maganganun da za su kawo rashin hadin kai tsakanin musulmi da al’umma baki daya, ya ce mafi yawancin mambobin kwamitin limaman masallatan Juma’a ne da ke da mutane a kalla 2000 da ke sallah a masallatan su.
“Suna da hanya mai sauki na haduwa da jama’a tare da isar da sakonni masu kyau ta hanyar tattauna abin a hudubarsu.” Ya yi kira ga dukkan yan takarar su taho su sanar da mutane shirye-shiryensu yana mai jadada cewa, “kwamitin ba ta goyon bayan kowanne dan takarar, kawai tana bawa kowa dama ne.” Ya yi kira ga yan siyasa su yi kamfen ba tare da tada hankula ba ko rikici ko furta maganganun da za su janyo tabarbarewar doka da oda.
You must log in to post a comment.