Kaduna: Majalisa Ta Yi Alwashin Taimakon Mata Masu Yaƙi Da Covid 19

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta sha alwashin taimakawa wa Ƙungiyar Mata masu yaƙi da cutar CORONA domin kai wa ga nasara akan ayyukan da suka sanya a gaba.

Shugaban Majalisar dokokin Jihar Kaduna Nasiru Zailani ne ya bayyana hakan, lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Matar a ziyarar da suka kawo a majalisar Dokokin Jihar a talatan nan.

Shugaban Majalisar wanda ya samu wakilicin mataimakin shi Honorabul Isaac Auta, ya ƙara da cewar nauyi ne wanda ya rataya a wuyan Majalisar taimakawa irin wadannan kungiyoyin domin shawo kan matsalar cutar a jihar Kaduna dama ƙasa baki daya.

Tun farko da take gabatar da jawabi jagorar Ƙungiyar Matan Dr. Lydia Umar ta bayyana cewar maƙasudin ziyarar tasu majalisar Dokokin Jihar Kaduna shine domin sanar da shugabannin Majalisar ayyukan kungiyar, da kuma neman goyon bayan su wajen isar da ayyukan kungiyar ga jama’ar jihar.

Dr. Lydia Umar ta kara da cewar akwai gagarumin aiki a garesu da bangaren hukumomi wajen ilimantarwa da wayar da kan jama’a akan illar cutar Covid 19, da kuma lalubo hanyar magance matsalar, sannan ta Jinjinawa majalisar dokokin Jihar Kaduna bisa kyakkyawar tarba da suka yi musu da alƙawarin da suka ɗaukar musu.

Labarai Makamanta