Kaduna: Majalisa Ta Sanya Kujerar Shagali A Kasuwa

Majalisar Dokokin jahar Kaduna ta bayyana kujerar tsohon shugaban majalisar Aminu Abdullahi Shagali dake wakiltar Sabon Gari, a matsayar wadda babu kowa akanta, biyo bayan karya dokokin majalisar na kin zuwa zaman majalisar har tsawon Kwanaki dari da ashirin.

Haka kuma majalisar ta dakatar da wasu yan majalisu guda hudu na tsawon shekara Guda, sakamakon kamasu da laifin cin amanar majalisar

Mutanen da majalisar ta dakatar sun hada da Mukhatar Isa Hazo dake wakiltar Basawa da Salisu Isa dake wakiltar Magajin Gari da Nuhu Goro dake wakiltar Kagarko sai kuma Yusuf Liman dake wakiltar Makera.

Labarai Makamanta