Kungiyar ‘yan Jarida ta ƙasa reshen Jihar Kaduna ta yi kira da babbar murya ga jam’iyyar PDP da ta gargadi jami’in yaɗa labarai na jam’iyyar a jihar Kaduna Katoh Alberah a ƙoƙarin da yake yi na raba kawunan ‘yan Jarida a jihar.
Kiran ya biyo bayan matakin da jami’in yaɗa labaran ya ɗauka na zaɓar wasu ‘yan Jarida a matsayin wadanda za su yi rahoto a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar da ke gudana a Kaduna da yin watsi da wasu ‘yan Jaridar.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba a Kaduna a taron karshen wata da kungiyar da ya gudana a Kaduna.
A cikin takardar bayan taron wadda ta samu sanya hannun Usman Sani ta bayyana matakin da Mista Katoh Alberah ke dauka a matsayin wani yunkuri na haifar da rarrabuwar kawuna tsakanin ‘yan Jarida a jihar.
Sanarwar ta bayyana jami’in yaɗa labaran a matsayin Mutum mai ɗagawa da nuna girman kai ga ‘yan Jarida a jihar.
Kungiyar ta shawarci ‘yan Jarida a jihar da su cigaba da gudanar da ayyukan su cikin tsari da haɗin kai da kauce wa dukkanin wani abu da zai kawo saɓani a tsakanin su.
“Matuƙar Mista Katoh Alberah zai cigaba da yin hakan babu shakka Ƙungiyar ba ta da wani zaɓi wanda ya wuce ta ƙauracewa ɗaukan labaran jam’iyyar PDP a Jihar.
Daga ƙarshe Ƙungiyar ta yi Allah wadai da cin zarafin da wasu jami’an tsaro suka yi wa ‘yan Jarida a yayin taron da Jam’iyyar PDP ta gudanar kwanan nan.
You must log in to post a comment.