Kotun daukaka kara dake zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da karan da Sani Sha’aban ya shigar kan nasarar dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani a zaben fidda gwanin gwamnan jam’iyyar da aka gudanar a jihar.
Kotun ta ce ta fahimci cewa, daukaka karar an yi ta ne ba bisa ka’ida ba, kuma bata cika abin da ake bukata na cancanta bisa dalilin haka ta yi watsi da ƙarar tare da tabbatar da nasarar Sanata Uba Sani.
Sha’aban ya daukaka kara ne kan hukuncin da babbar kotun tarayya mai zama a Kaduna ta yanke a ranar 4 ga watan Nuwamba, wacce ta yi watsi da kalubalantar zaben fidda gwanin, inda tace babu makama ko tushen gaskiya a batun.
Barista Sule Shuaibu, wanda shine lauyan APC ya tabbatar da cewa, an yanke hukuncin da ya ba Uba Sani gaskiya a zaben fidda gwanin da aka gudanar, zai ci gaba da rike tutar APC a matsayin dan takarar gwamna har zuwa zaben 2023.
Alkalai uku na kotun daukaka karan ne suka yi zaman yanke hukunci a ranar Laraba 13 ga watan Disamba.
You must log in to post a comment.