Kaduna: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Uba Sani A Takarar Gwamna

Babban kotun tarayya dake zamanta a Kaduna ta tabbatar da Sanata Uba Sani a matsayin sahihin dan takaran kujerar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyya mai mulki ta APC.

Alkalin kotun, Mohammed Garba, ya yi watsi da karar saboda kotunsa ba tada hurumin sauraron karar, a cewarsa. Garba ya ce wannan lamarin cikin gida ne tsakanin ‘yayan jam’iyya kuma ba matsalar zabe bace.

Honorabul Sani Sha’aban ne ya shigar da Uba Sani, jam’iyyar APC da hukumar INEC kotu kan zaben fidda gwanin dan takaran gwamnan jihar bisa zargin tafka maguɗi.

Sha’aban ya bukaci kotun ta soke zaben saboda an yi magudin Deleget. Yace tun daga matakin gunduma da karamar hukuma aka sauya sunayen deleget, masu gudanar da zaɓen fidda gwanin.

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ‘yan takarar gwamnan jihar Kaduna na ƙarshe da zasu fafata a babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Labarai Makamanta