Kaduna: Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa ‘Yan Bindiga A Zazzau

Matsalar ‘yan Bindiga da garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a kasarmu Najeriya musamman a yankin mu na arewa.

A Jihar Kaduna ma lamarin yaki ci yaki Cinyewa duk da kokarin da gwamnatin jihar keyi na shawo karshen matsalar.

Rahotannin dake shigowa jaridar muryaryanci.com a safiyar nan na nuna cewa a daren jiya litinin ne ‘yan bindiga suka kai hari a kofar kona dake karamar hukumar zariya. Amma Alhamdulillah Allah Ya ba jami’an tsaro galaba akan su sun rakasu da harbi Kuma sun ƙwato shanun da suka sace.

Ya zuwa yanzu wakilin muryar ‘yanci bai samu rahoton ko ansamu asarar rayuwa ko Kama daya daga cikin ‘yan Ta’addan da suka kawo harin ba .

wakilin muryaryanci.com ya tuntubi Jami’in yada labaran hukumar Yan sanda ta Jihar Kaduna domin jin ta bakinsu Amman hakan yaci tura domin lanbarsa baya shiga. Amman insha Allah zamu tuntuba mu kawo Maku cikakken rahoton nan bada jimawa.

Labarai Makamanta