Kaduna: Jami’an Tsaro Sun Tarwarsa Garken ‘Yan Bindiga

Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar haɗakar rundunar jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile harin yan bindiga a kan babbar hanyar Kaduna-Abuja a ranar Lahadi.

Dakarun Operation Puff Adder na hukumar yan sanda da haɗin guiwar rundunar Operation Thunder Strike na hukumar sojin Najeriya sun fatattaki yan bindigan tare da halaka wasu a sananniyar hanyar.

Kakakin hukumar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna, DSP Muhammed Jalige, a wata sanarwa, ya ce Dakarun tsaron sun tari yan ta’addan a yankin, inda suka yi musayar wuta. Sakamakon haka, jami’an tsaron suka yi nasarar cin ƙarfin su, hakan ya tilasta wa maharan tsere wa cikin jeji, yayin da aka aika wasu zuwa barzahu.

Jalige ya ce: “Yayin bincika wurin da aka yi gwabzawar, jami’ai sun gano bindiga AK-47 da Babura Tara na yan ta’adddan. Jami’an tsaro ba su gajiya ba a kokarin kare rantsuwar su ta kare rayukan matafiya da sauran masu bin hanyar.”

Kwamishinan ‘yan sandan Kaduna, Yekini Ayoku, ya nuna tsantsar jin daɗinsa bisa jajircewa da gwarzantakar jami’an tsaron, hakanan kuma ya tabbatar musu da cewa sadaukarwan su wajen kokarin kare rayuwar al’umma ya fi ƙarfin a saka musu da wani abu.

Kwamishinan ya ƙara da cewa yan ta’addan da aka jikkata yayin gwabzawar zasu bazama yankunan da ke yankin don neman a gyara musu raunukan su. Bisa haka, kwamishinan ya yi kira ga al’umma su gaggauta kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbi, inda ya tabbatar musu za’a kawo ɗauki nan take.

Labarai Makamanta