Kaduna: Jami’an KASTLEA Sun Kashe Direban Tifa Da Duka

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Jami’in kula da ababen hawa na Jihar KASTLEA, ya halaka wani direban Tifa a yayin rikici da ya shiga tsakaninsu a Ali Akilu Road, Unguwar Sarki, Kaduna a ranar Juma’a.

Lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 4 na yamma, ya janyo mummunan cinkoson ababen hawa a unguwar da kewaye.

Babu cikaken bayani game da abin da ya yi sanadin ricikin nasu a lokacin wallafa wannan rahoton, amma ganau sun ce an doki wanda abin ya faru da shi ne a kansa da wata katuwar sanda inda kan nashi ya fashe nan take.

Kakakin yan sandan Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige ya tabbatar da afkuwar lamarin, yana mai cewa Kwamishinan yan sandan Kaduna, Mudassiru Abdullahi ya bada umurnin a kamo wadanda suka aikata abin.

Ya kara da cewa yan sandan za su gudanar da cikaken bincike a kan lamarin. Ya ce: “An samu rashin jituwa tsakanin KASTLEA da wasu direbobi. Sun masa duka sannan aka garzaya da shi asibiti a can kuma ya ce ga garin ku. Don haka, wasu direbobin suka tare manyan hanyoyi domin zanga-zanga amma muka hana su.”

Rahotanni sun bayyana cewa a yayin da mutumin ya fadi kasa, Jami’an KASTLEA sun bar wurin saboda tsaron kada fusatattun matasa su kai musu hari.

Da aka tuntube shi, Shugaban KASTLEA, Mashal Garba Yahaya Rimi, ya ce bai riga ya samu cikaken bayani kan abin da ya faru ba don haka ba zai iya tsokaci a kai ba.

Labarai Makamanta