Kaduna: Iyalan Makarfi Sun Roki El Rufa’i Kan Karbe Musu Filaye

Rahoton dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Kamfanin Canes Properties Limited mallakin Tsohon Gwamna Makarfi ya rubuta wasika zuwa ga Mai girma Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a dalilin karbe masa filaye.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito ta bayyana cewa kamfanin ya roki Malam Nasir El-Rufai ya kara masa lokaci domin ya iya gina filayen da gwamnatinsa ta karbe.

Wasiku hudu da kamfanin na Canes Properties Limited ya aikawa Gwamna sun bada uzuri kan abin da ya hana a gine filayen tsawon shekarun da aka dauka. A game da fuloti da aka karbe mai lamba KDL 53874 a unguwar Mogadishu, kamfanin ya ce su na neman shekara guda domin gina rukunin shaguna.

Wasikar ta nuna an gabatar da takardar zanen ginin da za ayi, ana jiran amincewar KASUPDA. Wasika ta biyu ta nuna Makarfi zai bukaci karin watanni uku domin yin karin gine-gine a filayensa masu lamba: KDL 01868, KDL 79707 da kuma KDL 79709. Rahoton yace a game da sauran fulotin filin mai lamba KDL 264596, kamfanin tsohon Gwamnan ya na jiran takardun CofO daga hannun Gwamnatin Kaduna.

Labarai Makamanta