Kaduna: Isa Ashiru Ya Lashe Zaben Fidda Gwani A PDP

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tsohon ɗan majalisar wakilai mai wakiltar ƙananan hukumomin Maƙarfi da Kudan a majalisar wakilai Alhaji Isa Ashiru Kudan ya lashe zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP da babban rinjaye.

Alkaluman sakamakon zaɓen sun nuna cewar Isa Ashiru Kudan ya samu kuri’u mafiya rinjaye inda ya doke abokan takarar shi da samun kuri’u 414.

Tuni wasu daga cikin abokanan takarar tashi suka amince da kayen har suka miƙa sakon taya shi murna bisa ga nasarar da ya samu.

Tuni tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa Sanata Shehu Sani wanda kuri’a biyu rak a zaɓen ya wallafa sakon taya murna ga Isa Ashiru Kudan da kuma mika godiya ga Deligates da suka zaɓe shi ba tare ya basu ko sisi ba.

Labarai Makamanta