Kaduna: Harin ‘Yan Bindiga Ya Hallaka Mutane Bakwai

Gwamnatin Jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Gwamnan jihar Malam Nasiru Ahmad El Rufa’i a ranar Lahadi ta bayyana cewar wasu ‘yan bindiga sun halaka mutane bakwai a sassa daban-daban a jihar.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Samuel Aruwan ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a ranar Lahadi a Kaduna.

Aruwan ya ƙara da cewar “Cikin bakin ciki, jami’an tsaro sun bada rahoton cewa ‘yan bindiga sun kai wa wasu mutane hari a kauyen Kajinjiri da ke karamar hukumar Igabi inda suka kashe mutane biyu.” Ya ce wani mutum daya ya samu ranuka sakamakon harbinsa da bindiga da suka yi kuma ana jinyarsa a wani asibiti.

“Kazalika, a kauyen Rago da ke karamar hukumar Igabi, ‘yan bindiga sun kashe mutanen garin biyu,” in ji shi. Ya yi bayanin cewa a wani harin daban, ‘yan bindiga sun kai hari Kutura Station, Karamar hukumar Kajuru, sun kashe mazauna garin uku.

Kwamishinan ya ce Gwamna Nasir El-Rufai ya yi bakin cikin samun rahoton ya kuma yi wa iyalan wadanda suka rasu ta’aziyya tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu. Ya kuma yi wadanda suka jikkata sakamakon harin Kajinjiri fatan samun sauki cikin gaggawa.

Labarai Makamanta