Kaduna: Gwamnati Ta Bada Umarnin Buɗe Makarantu

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da umurnin ci gaba da koyar da daliban jihar gabadayan su. A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta hannun Kwamishinin Ilimin jihar Shehu Usman Muhammad a yammacin ranar Jumma’a gwamnatin jihar ta ce daga ranar Litinin 22.02.2021 ta bayar da izini ga daliban Nursery da Furamare da Sakandaren da a baya ta hana su komawa makaranta da cewa su koma ba tare da bata lokaci ba.

Sanarwar ta ce izinin da gwamnati ta bayar ya shafi makarantun kwana da na jeka dawo na gwamnati da kuma makarantun kudi har ma da Islamiyyoyi, dukkansu an amince musu su dawo da harkar koyarwa daga aji daya har zuwa ajin karshen.

Sai dai kuma gwamnatin ta ce wajibi ne makarantun su rinka daukar matakan kariya daga corona domin gwamnatin za ta rinka tura kwamiti na musamman da zai rika tabbatar da cewa makarantun na bin ka’idojin takaita corona.

Labarai Makamanta