Kaduna: Gwamnati Ta Ƙaddamar Da Shirin Kyautata Rayuwar Talakawa

Gwamna Nasir El-Rufai yau Talata, 23 ga watan Fabrairu 2021 ya kaddamar da wani shiri na musamman da zai kyautata rayuwar talakawa da marasa galihu a nan Gidan Gwamnati na Sir Kashim Ibrahim.

Malam Nasir El-Rufai a jawabinsa ya ce, tun da gwamnatinsu ta zo a shekara ta 2015 ta yi dokoki da tsare tsare na ganin ta inganta rayuwar talakawa da kuma marasa galihu a jihar. “tun zuwan wannan gwamnatinmu a shekara ta 2015 mun yi dokoki kuma mun kaddamar da shirye-shirye na ganin mun inganta rayuwar talakawa da marasa galihu a Jihar Kaduna.

A Jihar Kaduna mun mayar da ilimi daga matakin firamare zuwa sakandare kyauta don ganin kowane dan talaka ya samu damar zuwa makaranta. Sannan mun yi doka mai suna ‘Child right protection law’ wanda za ta kare hakkokin yara.

Bugu da kari, mun kaddamar da wani shiri na tallafa wa mata da nakasassu da bashin kudi don yin sana’o’i wanda muka fara da Naira miliyan dari biyu a shekara ta 2018.

Haka kuma mun kaddamar da shirin Inshorar Lafiya ta Jihar Kaduna da kuma shiri na bayar da kiwon lafiya ga kananan yara da mata masu ciki kyauta don inganta rayuwar talakawa da marasa galihu.

Sannan mu ne jiha ta farko da muka fara biyan mafi karancin albashi na Naira dubu talatin, kuma muka mayar da mafi karancin fansho zuwa Naira dubu talatin.

Sannan a kokarin da muke yi mu ga mun kyautata rayuwar talakawa da marasa galihu za mu bude ma’aikata ta musamman don ganin ta lura da wannan shiri da muka kaddamar yau na Kyautata Rayuwar Talakawa da Marasa Gaalihu a Jihar Kaduna.”

Saude Atoyebe, Jami’ar Kula da Shirin Kyautata Rayuwar Al’umma ta Jihar Kaduna ta bayyana cewa wannan shirin zai taimaka matuka wurin zakulo mutane masu bukatuwa ta musamman da tallafa musu don ganin an kyautata raywarsu. Haka ita ma Kwamishinar Ma’aikatar Kula da Walwalar Al’umma ta Jihar Kaduna a jawabinta ta bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wa marasa galihu matuka, kuma ta jinjina wa Gwamna El-Rufai kan wannan yunkuri.

A bangaren abokan huldar Jihar Kaduna kuwa, kungioyi masu zaman kansu kamarsu UNICEF, Save The Children da sauransu sun jinjina wa Gwamnatin Jihar Kaduna na kaddamar da wannan shirin don zai taimaka matuka a kokarin da gwamnatin ke yi wurin ganin ta kyautata rayuwar talaka.

Labarai Makamanta