Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar hukumar Ilimi bai ɗaya ta Jihar Kaduna, KADSUBEB, ta ce ta kori malamai 2,357 wadanda suka fadi jarrabawar cancanta da aka gudanar a baya-bayan nan
Mai magana da yawun hukumar, Malama Hauwa Mohammed cikin wata sanarwa da ta fitar, a ranar Lahadi a Kaduna ta ce hukumar ta yi wa fiye da malamai 30000 gwajin cancantar a watan Disambar 2021.
Ta ce an kori malamai 2,192 na Firamare ciki har da shugaban kungiyar malamai na kasa, NUT, Mr Audu Amba, saboda kin rubuta jarrabawar ta cancanta. Ta ce an sallami malamai 165 cikin 27662 da suka rubuta jarrabawar saboda ba su ci ba.
You must log in to post a comment.