Kaduna: El Rufa’i Ya Gabatar Da Kasafin Kudi

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Gwamna Malam Nasiru El-Rufai ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2022 na naira biliyan 233 ga majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Talata 12 ga watan Oktoba.

Kasafin kudin yana dauke da bayanin kashe Naira biliyan 146 a fannin ayyuka da jari da kuma na Kashewa akai-akai da suka kai Naira biliyan 87.6 a shekarar.

El-Rufa’i ya yi nuni da cewa rabe-raben da aka yi a cikin alkaluman kasafin kudin na shekarar 2022 sun yi nuni da kimar siyasa da ka’idojin shugabanci wanda a koda yaushe suke jagorantar kasafin kudi shida na baya da gwamnatinsa ta gabatar.

El Rufa’i ya ce alkaluman shekarar 2022 sun yi kasa da kasafin kudin 2021 na N237.52bn, wanda ke da N157.56bn na ayyuka da jari da kuma N79.96bn da aka tsara don kashewa akai-akai, kashi 66% zuwa 34% na jarin da ake samu.

A sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar a shafinta na Facebook, gwamnan ya bayyana cewa abubuwan da aka sa a gaba na kasafin 2022 sun hada da Ilimi, Kiwon Lafiya da Kayayyakin more rayuwa, kamar dai na kasafin baya.

Gwamnan ya kuma mika godiyarsa ga majalisar dokokin jihar bisa goyon baya da suke ba gwamnatinsa da ta dukufa wajen ayyukan ci gaba da al’ummar jihar ta Kaduna.

Labarai Makamanta