Kaduna: El Rufa’i Ya Fatattaki Muƙarraban Gwamnatinshi 19


Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya amince da korar masu taimaka masa na musamman guda 19 daga aiki.

A cewar wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a yau Laraba, wannan ne zagayen farko na masu muƙamana siyasa da za a kora a yunƙurin da gwamnan ke yi na rage yawan ma’aikatan gwamnati.

Daga cikin waɗanda aka kora akwai mataimakin shugaban ma’aikatan gidan gwamnati da babban darakta a hukumar Public Procurement Authority.

Gwamna El-Rufai ya sha suka game da korar ma’aikata kusan 7,000 da ya yi, abin da ya jawo yajin aikin ma’aikata na kwana huɗu a jihar.

Sai dai gwamnatin na kare matakin da cewa tana kashe kusan kashi 80 cikin 100 na kuɗin da take samu wajen biyan albashi.Article share tools

Labarai Makamanta