Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kama wani mai rike da sarautar gargajiya a masarautar Zazzau da aka sakaya sunansa a Zariya bisa zargin yin luwadi da wani yaro dan shekara 14.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Muhammadu Jalige, ya shaida wa manema labarai a Zariya, jihar Kaduna a ranar Laraba, inda ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin idan aka kammala bincike.
Yayan yaron, Hamza Zubairu, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Disamba a Unguwar Kwarbai da ke Zariya.
Mista Zubairu ya ce wanda ake zargin, makwabcin iyayen yaron ne ya kasance yana girmama su sosai a unguwar.
Ya kara da cewa a ranar da lamarin ya faru, wanda ake zargin ya aika wanda abin ya shafa cikin dakinsa domin ya dauko kudi amma ya bi matashin cikin dakin ya kulle kofa.
Daga baya mai wannan laifin ya zare wuka kuma ya yi barazanar kashe yaron idan yai ihu kan abin da zai yi masa.
Ya ce yaron ya shiga damuwa kuma bai iya gaya wa kowa abin da ya faru da farko ba har sai da ya samu kwarin gwiwa ya gaya wa innarsa.
“Goggon ce ta kai rahoton lamarin ga ‘yan sanda a hedikwatar ‘yan sanda ta birnin Zariya,” inji Mista Zubairu.
A nata jawabin, Aishatu Ahmed, Ko’odineta, Salama Sexual Assault Referral Referral Centre, Gambo Sawaba General Hospital, Zaria, ta shaida wa NAN cewa cibiyar ta samu bukatar kulawar lafiyar wanda abin ya shafa.
Ta ce cibiyar ta aike da sakamakon bincikenta zuwa hedikwatar ‘yan sanda na birnin Zariya.
You must log in to post a comment.