Kaduna: Dillalin ‘Yan Bindiga Ya Shiga Hannu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta ce jami’anta sun kama wani dan fashin jeji kuma mai safarar bindigu tare da kwato bindigogi kirar AK47 guda hudu da alburusai 344 da kuma babur din sa a Kaduna.

Kakakin rundunar, Muhammad Jalige ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya fitar yau Lahadi a Kaduna.

Jalige ya bayyana cewa, a ranar 23 ga watan Disamba, da misalin karfe 17:30 na safe, jami’an tsaro da ke Tudun Wada Zaria, a yayin da suke sintiri a Kwarkwaron Manu, unguwar Basawa, cikin birnin Zariya, sun kama wasu mutane biyu a kan babur mara lamba, ɗauke da jakunkuna a boye kuma suka nuna rashin gaskiya.

“Da aka tsare su domin bincike, ɗaya fasinjan babur din ya tsallake ya tsere, wanda hakan ya kara nuna shakku ga jami’an da suke sintiri.

“nan da nan a ka fara bincikar babur ɗin da matukin, wanda ya bayyana sunan sa da Bilyaminu Saidu mai shekaru 33 a kauyen Shuwaki da ke karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina, inda hakan ya kai ga kama shi.

“Kayan da aka kama sun hada da bindigogi kirar AK47 guda hudu, harsashi 344 mai tsayin 7.62mm, wayoyi da kuma layu,” in ji shi.

Mista Jalige ya ce wanda ake zargin an kai shi gidan yari kuma bincike na farko ya nuna cewa shi da abokin sa da ya gudu na da wata mummunar manufa ta safarar makamai ga ƴan kungiyar sa.

Jalige ya ce kwalliya ta biya kuɗin sabulu a sabon kwazo da hafsoshi da jami’an rundunar tsaro ke yi.

Labarai Makamanta