Kaduna: Dakarun Soji Sun Tarwatsa Sansanin ‘Yan Bindiga

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Dakarun rundunar sojoji na 1 Division sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga tare da kama wasu da dama a ranar Litinin.

Mai magana da yawun rundunar sojoji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya tabbatar da lamarin cikin sanarwar da ya fitar a shafin Twitter na rundunar a ranar Talata.

A cewar sanarwar, GOC na 1 Division, Nigerian Army, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ne ya jagoranci tawagar da ta kai samamen tare da hadin gwiwan wasu kwamandoji.

Nwachukwu ya ce: “Dakarun sojoji sun yi nasarar fatattakar yan bindiga a garuruwan Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello da Dogon Dawa a Jihar Kaduna, yayin wani sintiri da suka fita a ranar Litinin.

“A musayar wutan da aka yi, sojojin sun ci galaba kan yan bindigan, suka halaka da dama daga cikinsu, yayin da aka kama uku da ransu kuma wasu sun tsere da raunin bindiga.

” Nwachukwu ya cigaba da cewa: “Tawagar sojojin sun kuma kwato bindigu AK-47 harsashi mai tsawon 7.62mm da babura 18.” Daga karshe ya yi kira ga al’umma su lura da cibiyoyin lafiya, su kai rahoton duk wani da aka gani ya zo da raunin bindiga yana neman a yi masa magani, su kai rahoto ga hukumomin tsaro da suka dace.

Labarai Makamanta

Leave a Reply