Kaduna: Bankin Duniya Zai Gina Makarantu A Fadin Jihar

Getty Images

Shirin Bankin Duniya na samar da ilimi ga ‘yan mata zai gina makarantun sakandire daga aji daya zuwa uku guda 90, zai kuma gina daga aji hudu zuwa shida guda 69, ya kuma gyara 69 da suka lalace a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.

Shugaban shirin AGILE a jihar, Habibu Alhassan ne ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya hakan a Kaduna a ranar Laraba.

Yace shirin na tsawon shekara biyar an kirkiro shi ne domin tabbatar da cewa yara mata daga tsakanin shekara 10 zuwa 20 sun samu karatun sakandire.

Yaka kara da cewa gina sabbin makarantun da kuma gyara wadanda suka lalacen wani yunkuri ne na samar da wani tsarin da zai kara ba su damar koyo a rayuwarsu.

Labarai Makamanta