Kaduna: An Yi Nasarar Hallaka Kwamandan ‘Yan Bindiga Ali Dogo

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar Dubun Shugaba kuma gagararren ‘dan ta’addan jihar Ali Dogo, ta cika inda sojoji suka aika shi lahira tare da wasu mayakansa sakamakon luguden wuta ta jiragen yaki da aka yi musu a karamar hukumar Giwa ta jihar.

Wata majiyar tsaro ta sanarwa PRNigeria cewa Dogo da mabiyansa sun tsero daga jihar Niger zuwa karamar Hukumar Giwa ta jihar Kaduna sakamakon luguden wutan da aka matsanta musu a maboyarsu.

‘Yan ta’addan sun samu maboya ne a gidan wani Alhaji Gwarzo a Yadi dake karamar hukumar Giwa kafin a halaka su. Majiyar tace: “Abun takaici ga Dogo da mayakansa, yayin da suke taro, jiragen NAF sun yi lugude a gida Alhaji Gwarzo inda duk wanda yake gidan aka halaka shi har da Dogon.”

A wani bangare, luguden wuta mabanbanci da aka yi shi kan wani sansanin ‘yan ta’addan dake da nisan kilomita 33 arewa maso yamma na Mando a jihar Kaduna, ya zama ajalin wasu ‘yan ta’addan.

“Bayan bayyanan sirri kan cewa shugabannin ‘yan ta’addan da sojojinsu suna taro a karkashin bishiyoyi a wurin, an kai wa yankin samame wanda hakan yayi ajalin ‘yan ta’addan masu tarin yawa.”

Labarai Makamanta