Kaduna: An Yi Kiran Kwace Takarar Gwamna Hannun Hunkuyi A NNPP

Labarin dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewar hadakar kungiyoyin matasa a jam’iyyar NNPP Jihar Kaduna sun yi kira ga shugabannin jam’iyyar na kasa su canja dan takarar gwamnan jihar, Sanata Suleiman Hunkuyi.

Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takardar korafi da ta mika wa Ben Bako, shugaban jam’iyyar NNPP na jihar kan zargin da suke yi wa Sule Hunƙuyi.

Kungiyar ta yi ikirarin cewa Hunkuyi yana yi wa jam’iyyar APC ne aiki, ta kara da cewa har yanzu akwai damar a canja ‘yan takara. Takardar korafin ta ce: “Dan takarar gwamnan mu yana da halin hawainiya na ‘soyayya’ da abokan hamayyar mu a jihar, mafi yawancin mabiya jam’iyyar ba su gamsu da wannan abin da ya ke yi ba don haka zai janyo mana matsala.”

Takardar ta cigaba da cewa: “Muna tsoron dan takarar mu ya riga ya sayarwa jam’iyyar APC takararsa, tunda an san shi da yaudara a tarihin siyasar Kaduna. “A matsayinsa na dan takarar gwamna, ya kamata ya zama mai hada kan sauran yan takara, amma shi ke raba kan sauran yan takara wanda hakan cin amanar jam’iyya ne.

“Dan takarar gwamnan mu ya yi amfani da karfin ikonsa ya hana yan takarar da suka cancanta samun tikiti a zone I da zone II na jihar, ya zabi yan takara wadanda APC za ta iya kayar da su cikin sauki.

A bangarensa, Hukunyi ya ce wannan wasan kwaikwayo ne kawai. Ya ce an dauki nauyin matasan ne su bata masa suna da zargin da ba a iya tabbatarwa ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply