Kaduna: An Daina Ganin Ɗan El Rufa’i A Makarantar Gwamnati

Rahotanni daga Jihar Kaduna na bayyana cewar tun bayan da aka koma karatu a wannan zangon, Abubakar El-Rufai, dan gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, bai koma makaranta ba, kamar yadda sauran ‘ya’yan talakawa suka koma.

Indai jama’a basu manta ba a shekarar 2019, gwamna El-Rufa’i ya kai yaronsa makarantar Kaduna Capital School bayan alkawarin da yayi na cewar zai kai ɗaya daga cikin ‘ya’yan shi makarantar Gwamnati idan ya lashe zabe a shekarar 2019.

An samu labarin cewa rashin zuwan yaron makaranta ba zai rasa alaka da matsalar tsaro da garkuwa da daliban makaranta da akeyi a jihar Kaduna da sauran jihohin Arewa ba.

A ranar Litinin, wasu dalibai da Malaman makarantar sun bayyanawa wakilin SaharaReporters cewa Abubakar El-Rufa’i bai dawo makaranta ba tun da aka fara sabon zango.

Daya daga cikin daliban yace: “Ya daina zuwa. Ba na ganinsa. Ban sani ko har yanzu dan makarantar nan bane.” “Ajinsa na gidan benen nan, sashen daliban firamare. Amma bai zo makaranta ba tun da muka dawo,”

“Ka san matsalar tsaro a makarantun gwamnati a jihar; da yiwuwan iyayensa sun cireshi don gudun abinda ka iya biyo baya idan aka sace yara,” inji wani malami a makarantar ya fada.

“Kila iyayensa sun sa shi wata makarantar, kila kuma ya dawo, bayan makarantu sun samu tsaro. Saboda haka da yiwuwan ya yanke shawaran kare ‘dansa,”.

Labarai Makamanta