Kaduna: Allah Ya Yi Wa Sarkin Lere Rasuwa

Rahotanni daga Masarautar Lere dake jihar Kaduna na bayyana cewar Allah ya yi wa Sarkin Lere na 13 janar Abubakar Mohammed II rasuwa da safiyar ranar asabar, bayan gajeruwar rashin lafiya da yayi fama da shi.

” Tun da ya tashi ba ya jin dadi da safen yau sai aka dauko shi zuwa Kaduna, amma kuma ko da aka iso sai likita ya tabbatar da cewa Allah ya masa rasuwa”

Sarki Abubakar ya gaji babban wan sa Sarki Umaru Mohammed, wanda ya rasu a shekarar 2011.
Ya rasu ya bar ya’ya hudu da mata biyu.

Kafin sarki Abubakar ya dare kujerar sarautar Lere, ya rike mukamai da dama a Najeriya da suka hada da, gwamnan sokoto a 1985, sannan ya yi shugaban KADCCIMA a Kaduna.

” Marigayi sarki Abubakar II ya goya ‘ya yan yan uwa da karfafa zumunta a tsakanin mutanen masarautar Lere kafin Allah ya yi masa rasuwa.” In ji Mal Hussaini Mohammed.

Allah ya ji kan sa ya kuma gafarta masa ,Amin.

Labarai Makamanta