Kaduna 2023: Uba Sani Ne Zabin Mu – Al’ummar Karamar Hukumar Kubau

Dan takarar Gwamnan jihar Kaduna a jamiyyar APC Sanata Uba Sani ya sanar da cewa, gwamnatin jihar Kaduna kawai bata yi kasalandan a cin gashin kananan hukomomi 13 da ake da su a jihar ba.

Uba ya bayyana hakan ne a garin Anchau da ke a karamar hukumar Kubau, inda ya yi alkawarin ci gaba da gudanar da gagarumin ayyukan ci gaba da gwamnatin El-rufai ta gudanar a jihar a cikin shekaru 8 na mulkin jihar.

Sanatan wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar a yau bayan kammala ganawa da alummar ta Kubau a yau laraba ya ci gaba da cewa, a saboda cin gashin da shugabanin kananan hukomomin suka more ne, ya sa suka samu sukunin shimfida manyan ayyuka da dama a kananan hukomomin da suke shugabanta.

Ya yaba wa shugaban karamar hukumar ta Kubau , Alhaji Suleiman Zuntu, akan samar wa da alummar sa romon dimokiradiyya.

Da yake mayar da amsa akan bukatar gina dam a yankin, musamman don a kara bunkasa noman rani a yankin Uba, ya yi alkawarin cewa, ba wai gina dam kawai ba, in ya lashe zaben, zai kuma taimaka wa manoman yankin da kayan aikin noma kamar su takin zamani da ingantaccen Iri da sauransu.

Ko a makon da ya gabata, dan takarar ya gana da wasu manoma Pambegua, inda suka tattauna akan yadda za a kara habaka fannin aikin noma a yankin

A cewarsa, ya lura duk jawaban da jama’a suka gabatar a taron na ganawar, jinjina da kuma Allah san barka ne akan shugabancin adalci da gwamnatin El-rufai ta wanzar a jihar ne, inda ya ya yi alkawarin ci gaba da wanzar da tsare-tsaren da gwamnatin jihar ta faro in ya kai ga gaci.

Uba ya ce, har yau ni dalibi ne a gwamnatin Mal Nasir El-rufai, inda ya ce, na shafe shekaru 20 a cikin wannan makarantar har yanzu ba a yaye ni ba.

Ya kuma yi alkawarin ci gaba da yiwa kowanne dan jihar adalaci kamar yadda El-rufai ya ke ci gaba da yiwa alummar jihar, inda ya yi nuni da cewa, tun lokaci da gwamnatin El-rufai ta zo, ba a samu wani rikicin addini ba.

Labarai Makamanta