Ka Yi Gaggawar Sauya Fasalin Tsaro – Dattawan Arewa Ga Buhari

Kungiyar dattawan arewacin Najeriya Wand a ake kira northern elders forum (NEF) ta kara jaddada kira ga shugaba Buhari ya sauya fasalin tsaron kasar nan tare da sauke dukkan shuwagabannin tsaron.

Kungiyar ta bayyana hakan ne ta bakin daraktan yada labarai na kungiyar dattawan arewa Dr Hakeem Baba Ahmad.

Tabbas akwai kura kurai a yadda jami’an ‘yan sandan kasar nan ke gudanar da ayyukan su Amman kamata yayi ayi masu gyare- gyare na musamman wurin gudanar da ayyukan su tare da Sanya wasu daga cikin amintattun mutanen kasar nan domin bibiyar yadda suke gudanar da ayyukan su.

” Hakeem yace kamar yadda gwamnatin tarayya ta nuna damuwarta kan masu kiraye kirayen kawo karshen rundunar SARS cikin kankanin lokaci. Haka ya kamata gwamnatin ta nuna damuwarta akan yan bidigar da suka addabi yankin arewacin kasar nan, masu garkuwa da mutane, masu sace dabbobin makiyaya da sauran su.

An sha cin zarafin mutanen yankin arewacin kasar nan tun a lokacin gwamnatin baya dana yanzu ba tare da gwamnatin ta dauki wani matakin azo a gani ba. Kuma muddin anason zaman lafiya ya zama wajibi gwamnati ta kasance mai adalci ga kowane bangare na kasar nan ”inji Hakeem

Daga karshe kungiyar dattawan arewa tayi kira na musamman ga mutanen arewacin kasar nan akan su kasance yan kasa na gari masu bin dokokin da gwamnati sau da kafa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply