Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Ka Fallasa ‘Yan Majalisar Da Suka Amshi Kwangila – Majalisa Ga Ministan Neja Delta

Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila ya bawa Ministan Harkokin Niger Delta, NDDC, Godswill Akpabio, waadin awa 48 ya wallafa sunayen yan majalisa zubi ta 9 da suka karbi kwangila daga NDDC.

Shugaban ya yi wannan jawabin ne lokacin da ya ke martani a kan batun da shugaban marasa rinjaye, Ndudi Elumelu ya gabatar masa.

Mr Elumelu ya bukaci Majalisar ta gayyaci Mr Akpabio ya bayyana sunayen wadanda suka karbi kwangila daga NDDC.

Mr Akpabio a ranar Litinin yayin zaman sauraron baasi game da binciken zargin rashawa a NDDC ya yi ikirarin cewa NDDC na bawa yan majalisa kwangila.

Wannan batun ya tayar da hankula a wurin taron har sai da shugaban taron, Thomas Ereyitomi ya lalashe wasu yan majalisa da suka fara cacan baki da ministan.

Da ya ke martani a kan batun da Mr Elumelu ya gabatar masa, Kakakin ya ce bai ji dadin yada yan jarida suke taya shi yayata “abinda muka san ba gaskiya bane.”

“Ban taba karbar kwangila ba ko sau daya daga NDDC kuma na san wasu yan majalisar da dama kamar ni,” in ji Gbajabiamila.

“Saboda haka ina kira ga ministan ya wallafa sunayen yan majalisun, kwangiloli, kwanan wata da kamfanonin da ya ce an bawa kashi 60 na kwangilar ta hukumar NDDC.”

Ya ce idan ko ministan bai wallafa sunayen ba majalisar ba ta da wani zabi da ya wuce su dauki matakin da doka ta tanada a kan shi.

“Haka ta rataya a kan ministan, ya sanar da kwamitin, mutanen Niger Delta da yan Najeriya wadanda aka bawa kwangilolin,” a cewar Kakakin.

Exit mobile version