Ka Fada Mana Manufarka A Zaben 2023 – Walid Jibrin Ga Gwamna Bala

Daga Adamu Shehu Bauchi

Kafito fili ka fada mana manufarka da aniyan ka a zaben gama gari na shekarar 2023, mu kuma zamu goya maka baya a duk abinda kake so, Inji shugaban kwamitin amintattu na babban jamiyyar adawa ta PDP, Sanata Walid Jibrin, ya gaya ma Gwamnan jihar Bauchi Bala Abdulkadir Mohammed.

Shugaban ya fadi haka ne a Karamar hukumar Dambam cikin Jihar Bauchi, a lokacin da yake kaddamar da sabon Babban Asibitin Dambam a ranar laraba,

Sanatan Jibrin wanda shine babban Bako a wajen taron yace Gwamnatin jijohin pbp suna aiki tukuru, kana yace Kauran Bauchi mutanen Bauchi za suyi alfahari da irin ayyukan alheri da yake shimfidawa, kamar bangaren gina hanyoyi, fanin noma, da Kuma bangaren kiwon lafiya.

A lokacin jawabinsa Gwamnan jihar Bala Abdulkadir Mohammed yace ginin asibitin ya lakume kimanin naira Miliyan dari Uku da talatin N330, yace gwamnatinsu ta himmatu wajen aiyukan more rayuwa,

Bala ya kara da cewa wan nan zuwa da shugaban kwamitin amintattu na Jam’iyyar PDP yayi, yace manuniya ce da gamsuwa da irin ayyukan da muke aiwatar wa don gina al’umma, tare da walwala.

Asibitin dai angina shi ne da kayan aikin irin na zamani da gadajen haihuwa da dakin aikin agajin gaggawa na motar daukan marasa lafiya.

Labarai Makamanta