Ka Da Ku Sake Zabar Mijina Idan Ya Gaza A Zangon Farko – Matar Tinubu

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Matar dan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar APC, Oluremi Tinubu, ta shawarci ‘yan Najeriya su fatattaki Mijinta daga gadon mulki bayan shekaru hudu idan har aka zabe shi bai yi abinda ya dace ba.

Tinubu ta yi wannan furuci ne a Ralin mata na tallata Tinubu/Shettima a shiyyar kudu maso gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin jihar Imo.

“Mu jingine batun addini a gefe, ni kirista ce shin kun taba tunanin watarana za’a jaraba tikitin Kirista da Kirista? Wai me asalin zancen ne, mun taÉ“a jaraba Musulmi da Musulmi to ku bari mu fara jaraba wannan.”

“Kuma bayan shekaru hudu, idan har ba su kawo sauyi mai kyau ba, zaku iya canza su daga kan mulki,” inji mai dakin Tinubu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sanatar ta bayyana cewa bai kamata a zaben Najeriya a tsaya ana kace-kace kan imanin mutane ba, kamata ya yi mutane su natsu su É—auki dan takara mai tsoron Allah. Ta ci gaba da cewa: “Idan kuka samu mutum mai tsoron Allah, ba wai Kirista, Musulmi ko Katolika ba, mai tsoron Allah. Idan mai tsoron Allah ne a gadon mulki zai muku abinda ya dace.”

Oluremi Tinubu, wacce ta bayyana cewa ta yi aiki a matsayin matar gwamna da Sanata, ta tabbatarwa mata cewa zasu samu gurbi mai tsoka a gwamnatin Tinubu da Shettima.

“Wannan lokaci ne na yi wa Najeriya aiki babu zancen wasa. Batun mata, zamu tuna da ku kuma ika tabbatar masu da cewa Asiwaju zai tuna da ku. Tinubu da Shettima suna da kunshi na musamman ga matasa.”

Labarai Makamanta