Jonathan Ya Fi Ƙarfin Ɗaukar El Rufa’i A Matsayin Mataimaki – Omokri

Tsohon hadimin tsohon Shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya ce ko kaɗan mai gidansa ba zai taba yin takara tare da Gwamna Nasir El-Rufai ba, tsarin ba iri ɗaya bane Jonathan ya fi karfin yin takara da shi.

Ana rade-radin cewa tsohon shugaban kasar zai tsaya takara da Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a matsayin mataimakinsa a shekarar zabe mai zuwa ta 2023.

Reno Omokri ya na cewa Goodluck Jonathan bai da niyyar sauya-sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, ko kuma ya nemi shugaban kasa. Reno Omokri ya yi wannan bayani ne da aka yi hira da shi a wani shiri da ake kira The Roundtable.

Omokri wanda ya yi aiki a matsayin mai ba Goodluck Jonathan shawara a lokacin da yake mulki ya ce duk jita-jitar komawar Jonathan APC ba gaskiya ba ne. “Su na yada wannan labari ne saboda su saida Nasir El-Rufai a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa.”

“Na yi magana da Jonathan kafin wannan hirar. Labarin nan karya ne, ku ce ni ne na fada. ‘Idan ma har tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya na da niyyar yin takara ba zai ɗauki El Rufa’i ba, kuma ko tunanin ya tsaya neman kujerar shugaban kasa ba ya yi.”

“Iyaka sani na Jonathan ba zai canza sheka ba. Jam’iyya guda kadai ya taba yi, shekararsa 63, kuma bai da tarihin canza jam’iyya. Mutum ne shi mai amana”.

Kwanaki kun ji tsohon shugaban kasan Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi bayani a kan batun tsayawa takara a 2023, hakan na zuwa ne bayan rade-radin da ake yi.

A cewarsa, ya yi wuri ya fara bayyana ra’ayinsa na tsaya wa takarar shugaban kasa. Ya ce ya kamata a maida hankula a kan wasu matsalolin da ke addabar kasar. Rahotanni sun ce akwai wasu gwamnonin APC huɗu da su ka matsa wajen zawarcin Jonathan.

Labarai Makamanta