Jonathan Dattijon Ƙwarai Ne – Buhari

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murnar cika shekaru 64 da haihuwa wanda ke zuwa a ranar 17 ga Nuwamba, 2021.

Shugaban, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata ta hannun mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ya taya shi murnar yi wa kasa hidima, da kuma kokarin tabbatar da zaman lafiya da ci gaban dimokuradiyya a nahiyar Afirka.

A cewar wani yankin sanarwar: “A madadin gwamnati da ‘yan Najeriya, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika gaisuwa ga tsohon shugaban kasa, Dr Goodluck Ebele Jonathan da murnar cika shekaru 64 da haihuwa, 17 ga watan Nuwamba, 2021.”

Buhari ya ce Jonathan ya ci gaba da fadada iyakokin shugabanci ta hanyar koya wa da dama daga cikin kasar karfin mayar da hankali, daidaito da kuma himma. Ya yaba yadda Jonathan ya zama mataimakin Gwamna, Gwamna, Mataimakin Shugaban kasa, Shugaban kasa, Wakilin Tarayyar Afirka, kuma yanzu ya zama Shugaban taron kasa da kasa Majalisar Amincin Afirka (ISCP-Africa) lallai shi Dattijon Ƙwarai ne.

Labarai Makamanta