Jirgin Yakin Neman Zaben Kwankwaso Ya Dira Kaduna

Rahoton dake shigo mana daga jihar Kaduna na bayyana cewa mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam’iyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya shawarci ‘yan Najeriya su guji zaben wasu jam’iyu musamman APC da PDP a zaben watan Fabrairu dake tafe.

Kwankwaso ya baiwa yan Najeriya wannan shawarin ne a wurin Ralin kamfe dinsa na arewa maso yamma da ya gudana a Jihar Kaduna.

Kwankwaso ya bayyana cewa akwai bukatar mutanen Najeriya su farga su fatattaki APC da PDP wadanda suka lalata Najeriya tsawon shekaru sama da 20.

“Bari na yi amfani da wannan damar na gaya maku mutanen arewa maso yamma da ma Najeriya baki daya cewa jam’iyyarmu NNPP wuyanta ya kai tsara, mun shiga kowace gunduma a kasar nan.”

Tsohon gwanman jihar Kanon ya roki magoya bayan jam’iyyar NNPP su tashi tsaye su yi aiki tukuru domin samun nasara a watan Fabrairu. A cewarsa, mulkin manyan jam’iyyu biyu watau PDP da APC da ya shafe shekaru 24 ya gaza mafi munin gazawa.

“Sun gaza tsinana komai a kasar nan kama daga bangaren tattalin ariziki, tsaro da manyan ayyukan raya kasa, sun gaza har a bangaren hada kan ‘yan Najeriya.” Kwankwaso ya ce jam’iyyar NNPP ce kadai mafita game da kalubalen da suka dabaibaye Najeriya sakamakon gurbataccen shugabanci a tsawon waɗannan shekaru.

Labarai Makamanta