Rahotanni daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wani ruwan bama-bamai da jirgin yakin rundunar Operation Hadarin Daji ya yi, ya hallaka adadi mai yawa na yan bindiga a yankin arewa ta yamma.
A rahoton PRNigeria, harin jirgin yakin, wanda sojojin sama suka aiwatar a Dangwandi da Tsakai dake karamar hukumar Isa, ya yi sanadin mutuwar ƙusoshin yan bindiga da dama.
Kazalika makamancin irin wannan ruwan bama-baman ta sama, ya hallaka kayayyakin amfani yan bindiga da yawan gaske a wasu sassan Zamfara.
You must log in to post a comment.