Jira Ya Kare: Daliban Jami’a Za Su Koma Darasi – Minista

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Ministan kwadago da samar da ayyuka Chris Ngige ya ce nan bada jimawa ba za a kawo karshen yajin aikin da malaman jami’a ke yi a kasar.

Ngige ya sanar da hakan ranar Laraba, yayin zantawa da manema labarai bayan kammala taro a fadar Shugaban kasa.

Ngige ya musanta zargin da ake yi wa gwamnatin tarayya na yin ko oho da korafe-korafen ASUU, inda ya tabbatar da cewa suna kan tattaunawa da Shugabancin kungiyar.

Ministan ya kara da cewa suna da wani zaman da ASUU ranar Alhamis, da zimmar kawo karshen tirka-tirkar don suga cewa dalibai sun koma azuzuwansu.

An shafe watanni daliban jami’o’i a Najeriya na zaune gida saboda yajin aiki, wanda ASUU ta shiga saboda zargin gwamnatin Najeriya da gaza biya mata bukatunta kamar yadda suka yi yarjejeniya a baya.

Labarai Makamanta