Jihar Jigawa Na Sahun Gaba A Yawan Adadin Yara Masu Fama Da Yunwa

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar kashi 65 cikin 100 na yaran Arewa maso Yamma suna fama da talauci da yawa, inda jihar Jigawa ke matsayi mafi girma, Kamar yadda binciken 2021 Multiple Indicator Cluster Survey (MICS 6) ya nuna.

Rahoton Mics 6 wanda aka kaddamar jiya a Dutse, kuma Ma’aikatar Kudi da Tsare Tattalin Arziki ta Jihar Jigawa tare da hadin guiwar ofishin UNICEF suka dauki nauyinsa.

Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki da dama da suka hada da shugabannin siyasa, ma’aikatan gwamnati, kungiyoyin jama’a, shugabannin al’umma, shugabannin gargajiya, malaman addini da sauran masu hannu da shuni.

Raham Mohammed Farah ta ofishin UNICEF na Kano ta ce binciken da aka gudanar a shekarar 2021 ya nuna cewa kashi 73.9% na yara a Jigawa matalauta ne. Wannan binciken ya nuna cewa a jihar Jigawa yara basa samun abubuwan more rayuwa. Galibin yara a jihar an tauye musu hakkinsu na rayuwa,da kuma ci gaba, injji Raham.

Rahoton ya kara da cewa, yayin da jihar ta samu ci gaba yakar cutar shan inna, daga shekarar 2011 zuwa 2021, sannan ta samu gaggarumin nasara raguwar mace-macen yara ‘yan kasa da shekaru biyar da kashi 37%. “Duk da haka, har yanzu akwai alamun da yara basu san me ake ba a jihar jigawa sabida rashin samun abunda suke bukata”.

“A fannin ilimi, kashi 44% na yaran da ya kamata ace su yi firamare ko sikandire ko makaratun fasaha ba su wuce kashi 2% a cikin 100% na yaran ba.” Yayin Kaddamar da Rahoton MICS6, Rahma ta yi kira na gaggawa ga shugabannin al’umma, kungiyoyin farar hula, ‘yan siyasa, ‘yan majalisar jiha da sauran masu ruwa da tsaki kan lamarin. Inda tace: “Ya kamata a fito da dabarun inganta yanayin ci gaban bil’adama a jihar musamman don inganta rayuwar yara da matan da suka fi fama da wahala,”

Labarai Makamanta

Leave a Reply