Jigawa: ‘Yan Bindiga Sun Hallaka Manyan Jami’an ‘Yan Sanda

Rahotanni daga Jihar Jigawa na bayyana cewar Rundunar ‘yan sandan jihar ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe wasu manyan jami’an ta biyu kuma sun yi garkuwa da sirikin wani babban dan kwangila a jihar.

Wannan abu dai ya auku ne a kauyen Kwalam dake karamar hukumar Taura.

‘Yan bindigan sun yi garkuwa da sirikin Haruna Maifata, Ma’aru Abubakar bayan sun kashe ‘yan sandan biyu dake sintiri a kauyen.

Kakakin rundunar Lawan Adam da ya tabbatar da haka wa manema labarai ranar Litini ya ce ‘yan bindigan sun kashe sufirtanda Anas Usaini da sifeto Sunusi Alhassan.

Labarai Makamanta