Jigawa: Sheikh Birnin Kudu Ya Samu Babban Mukami

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya nada sanannen malamin addinin musulunci Dakta Abubakar Sani Birnin Kudu a matsayin babban sakataren ma’aikatar ilmin addinin musulunci ta jihar Jigawa.

Kafin nadin Dr Abubakar Birnin Kudu, malami ne a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria. Kuma shine babban limamin masarautar Dutse babban birnin jihar Jigawa.

Sannan mataimakin darakta ne a ma’aikatar da aka nada shi a matsayin jagora a yanzu.

Sanarwar nadin ta fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Alhaji Adamu Abdulqadir Fanini Birnin Kudu.

Related posts