Jigawa: Matashi Dan Shekara 25 Ya Rataye Kanshi

Rundunar ƴan sandan Jihar Jigawa ta ce wani matashi dan shekara 25 ya kashe kansa a karamar hukumar Taura da ke jihar.

Kakakin Rundunar Ƴan sandan Jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Talata a Dutse, babban birnin jihar.

Shiisu ya ce matashin ya yi amfani da wandonsa ne ya rataye kanshi a jikin wata bishiya a jiya Litinin.

Ya ce, matashin, wanda a baya aka ce ya ɓace, an same shi yana rataye a jikin bishiya a wani daji da ke wajen kauyen Zangon Maje.

“A ranar 24 ga watan Janairu da misalin karfe 2:30 na rana Hakimin Kwalam, Alhaji Muttaka Uba ya kira waya ya shaida masa cewa wani Naziru Badamasi mai shekaru 25 a kauyen Tsadawa da ke karamar hukumar Taura kuma yana fama da taɓin hankali, ya ɓata tun bayan da ya bar gida da misalin karfe 12:30 na dare.

“An same shi ne bayan ya rataye kansa da wandonsa a kan wata bishiya a wajen kauyen Zangon Maje, da ke karamar hukumar Taura,” inji shi.

Shiisu ya kara da cewa, bayan samun bayanan ne tawagar ‘yan sanda su ka je wurin da lamarin ya faru, inda suka kai gawar zuwa babban asibitin Ringim, inda wani likita ya tabbatar da mutuwar ta.

A cewarsa, daga baya an sako gawar ga ’yan uwan ​​mamacin domin a binne shi saboda babu wani zargin ko kashe shi a ka yi bayan bincike na farko.

Labarai Makamanta