Jigawa: Matasa Sun Yi Wa Dan Majalisa Rajamu

Al’ummar mazabar ɗan Majalisar Wakilai ta Ƙasa mai wakiltar ƙananan hukumomin Birnin Kudu/Buji dake jihar Jigawa, Magaji Da’u, sun nuna fushinsu ga ɗan majalisar inda suka kai wa tawagarsa hari a garin Kukuma akan hanyarsa ta zuwa taron siyasa.

Al’ummar mazaɓar sun zargi ɗan majalisa Da’u da yin watsi dasu da tarewa a Abuja na tsawon lokaci.

‘Yan sanda sun shaida wa wakilinmu cewa ɗan majalisar yana kan hanyarsa ta zuwa wani taron siyasa ne a yankin lokacin da abin ya faru.

Maimagana da yawun Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, Lawan Adam, ya ce ba ‘yan bindiga ne suka kai harin ba, rashin fahimta ce kawai tsakanin wasu ɓangarorin siyasa ya haifar da harin.

“An shawo kan al’amarin kuma ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargi”, in ji Lawan.

Maharan sun tare hanyar da ɗan majalisar zai je ƙauyen Kukuma don halartar wani taron siyasa.

Al’ummar mazaɓar Da’u sun yi ta jifar sa da munanan kalamai, suna masu zargin sa da rashin yin kataɓus da kuma watsi da su har sai yanzu da zaɓen 2023 ya kusa.

Siyasa ta kunno kai yanzu, mutane na nan suna kakkabe katin zaɓen su. Wasu za su sha wasu kuma yadda hali ta yi.

Da yawa daga cikin ƴan siyasa sukan wancakalar da mutanen mazaɓun su ne idan suka ci zaɓe sai kuma lokacin neman ƙuri’un su yayi sai su fara lekowa gida akai akai suna sharar fage.

Labarai Makamanta