Jigawa: Jam’iyyar APC Ta Dakatar Da Honorabul Gudaji Kazaure

Rahotanni daga Jihar Jigawa na bayyana cewar Jam’iyya mai mulki ta APC, reshen karamar hukumar Kazaure ta dakatar da ɗan majalisa mai wakiltar mazabar Kazaure, Roni, Gwiwa da Yankwashi a majalisar wakilai, Muhammad Gudaji Kazaure.

Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar dakatarwa da aka rarraba wa manema labarai dauke da sa hannun shugaban jam’iyyar, na karamar hukumar Kazaure, Hassan Lawan.

Sanarwar ta ce an dakatar da dan majalisar tarayyar na tsawon watanni shida saboda wani rubutu da ake zarginsa da wallafawa a shafinsa na Facebook da Twitter a kan gwamnan jihar Muhammad Badaru Abubakar wanda ya saba wa doka ta 21 (ii) da (v) na kundin tsarin mulkin APC.

Sanarwar ta bayyana cewa dakatarwar ta biyo bayan dakatarwar da shugabannin yankinsa na Yamma suka yi a can baya. Hassan ya ce bisa koke-koken da aka karba daga yankin dan majalisar ne shugabannin zartarwar Jam’iyyar na Karamar Hukumar suka yi taron gaggawa kuma suka yanke shawara biyu.

Shawarwarin sun hada da kafa kwamitin ladabtarwa na mutum bakwai don bincikar zargin tare da gabatar da rahoto cikin kwanaki goma yayin da aka dakatar da dan majalisa na tsawon watanni shida har zuwa lokacin da za a gudanar da bincike.

A cikin rubutun nasa, Gudaji ya zargi Gwamna Badaru da gabatar da sunayen shugabanni da kansiloli ‘yan takarar zaben kananan hukumomi mai zuwa ba tare da zaben fidda gwani ba ko wata yarjejeniya kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyya ya jagoranta.

Labarai Makamanta