Jigawa: Hatsarin Jirgin Ruwa Ya Laƙume Rayukan ‘Yan Mata 7

Yara mata guda 7 ne, ƴan shakara 10 zuwa 12, su ka hallaka a wani haɗari na kwale-kwale da ya kife da su a kan hanyarsu ta zuwa bikin maulidi a ƙauyen Gamafoi, Ƙaramar Hukumar Kafin Hausa, Jihar Jigawa.

Jaridar Nation ta rawaito cewa ƴan matan su 10 ne su ke tafiya daga ƙauyen Gafasa zuwa Gasanya a karamar hukumar Auyo domin zuwa wajen maulidi a lokacin da ibtila’in ya faru.

Dagacin Gamafoi, Haruna Gamafoi ne ya kai rahoton haɗarin ga ƴan sanda.

Ya ce haɗarin ya faru ne wajen ƙarfe 3:30 lokacin da jirgin ya kife da ƴan mata goma amma an yi nasara tserar da uku daga ciki, inda bakwai su ka ce ga garinku nan.

An rawaito cewa ƴan matan suna sauri za su tafi garin ne kuma da suka zo gaɓar kogin Gasanya amma ba su samu mai fito ba shine su ka tuƙa kwale-kwalen da kan su.

Bayan haɗarin ya afku sai a ka garzaya da su asibitin Kafin Hausa inda likitoci su ka tabbatar da rasuwar 7 da ga cikinsu.

Rundunar Ƴan sanda ta Jigawa ta tabbatar da faruwar haɗarin.

Labarai Makamanta