Jigawa: Badaru Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kisa Ga Masu Fyaɗe

Mai girma Gwamna jihar Jigawa Alh. Muhammad Badaru Abubakar (mon,mni) ya saka hannu akan dokar hana cin zarafin dan Adam a jihar Jigawa guda shida.

Sannan kuma dokar ta fara aiki a yau, daga cikin abubuwan da dokar ta hana sune:

(1) Aikata fyade akan mace ko namiji, yaro ko babba, duk wanda ya aikata laifin zai dauki hukuncin kisa, daurin rai da rai babu tara.

(2) Wadda ya taimaka, ko shawara ko bada umarnin aikata fade za’a masa hukuncin kisa ko daurin rai da rai.

(3) Amfani da “yan jagaliyar siyasa zai dauki hukuncin mafi karanci daurin shekara 4 a gidan yari.

(4) Amfani da maganganun batsa, hotunan batsa domin tallar magani a cikin al’umma laifi ne kuma zai dauki hukun daurin wata 4 ko tarar #10,000.

(5) FGM batawa mata al’aura da sunan kaciya laifi ne kuma hukuncin daurin wata 3 ko tara ta #10,000.

(6) Garkuwa da mutane laifi ne kuma hukuncin kisa ne akan duk wadda aka kama.

Labarai Makamanta