Jigawa: Adadin Wadanda Ambaliya Ta Kashe Ya Kai 108

Rahotannin dake shigo mana daga jihar Jigawa na bayyana cewar adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta kashe a Jihar sun kai 108 tun daga watan Agusta.

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar ta ce akasarin mutanen sun rasu ne sakamakon nitsewa a ruwa da tsawa da kuma rushewar gine-gine.

Mai magana da yawun rundunar, Lawan Adam, ya bayyana a yau Asabar cewa an tattara adadin ne tun daga watan Agusta.

A gefe guda kuma, Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya nemi gwamnatin tarayya ta ayyana jiharsa a matsayin “wadda bala’i ya afka mata” saboda ambaliyar ruwan da ta fuskanta.

Labarai Makamanta