Wata jarumar Kannywood ta fito fili ta fadi abinda ya ke damun ta dangane da Saratu Gidado wacce aka fi sani da Daso a wani bidiyo da NaijaFamily su ka wallafa a shafin su na Facebook.
Jarumar wacce ba ta shahara kwarai ba ta bayyana takaicin ta da alhini akan yadda Daso ta ke kwasar rawa a shafin ta na TikTok inda ta ce ya kamata manyan Kannywood su fada ma ta gaskiya.
A cewar ta, Daso ta na zubar da mutuncin yaran ta, jikokin ta, zuriāar ta da kuma su āyan Kannywood don haka ya kamata ta gyara. Kamar yadda jarumar ta ce a farkon bidiyon: āDon Allah manyan Kannywood ku na nan? Ku na nan da ran ku da lafiyar ku ku na ganin abinda baiwar Allar nan ta ke yi? Ku na ganin tabargazar da ta ke yi wa mutane a TikTok?
āSai mu kananan yara ma su jini a jiki?, ko mu wallahi idan ance in yi abinda ta ke yi bazan iya ba. Jumaāa guda ke ba ki yi happy Jumaāa na karatu ba, ba ki yi na adduāa ba ki sa riga da wando ki dinga yi wa mutane rawa a TikTok?
āTa yi a falo, ta yi a location, ta yi a titi, ta yi a gida? Shi ke nan duk Kannywood an rasa wanda zai tsawatar ma ta?ā Ta ce a cire tsoro a yi wa Daso magana Ta ci gaba da cewa ya kamata ace an cire tsoro an fada ma ta gaskiya don ba wannan ne karon ta na farko da ta ke kwasar rawar ba a duba shafin ta, ta na rawar yadda ta ga dama.
Ta ce idan Daso ba ta kare mutuncin āyan Kannywood ba, ya kamata ta kare darajar yaranta da kuma jikoki da āyan uwa. A karshen bidiyon an san ya bidiyon da Daso ta ke sanye da bakaken riga da wando zaune a kujera ta na kwasar rawar wakar Dj AB ta āDan Lukutiā ta na jefa hannu tare da juya jikin ta.
You must log in to post a comment.