Jaruman Kannywood Sun Yi Mubaya’a Ga Takarar Tinubu

Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Manyan taurarin Kannywood, wadanda suka hada da Ali Nuhu, Adam Zango, Sadiq Sani, Rabi’u Daushe, da saura da dama, sun fito fili sun marawa ‘dan takarar shugaban kasar jam’iyyar APC, Bola Tinubu baya a babban zaben dake tafe na 2023.

An ruwaito cewa taurarin Kannywood din sun bayyana goyon bayan su ga Tinubu a zaben shugaban kasa na watan Fabrairu a yayin yaƙin neman zaɓe da ya gudana a birnin Kano.

Fitaccen jarumin Kannywood Adam Zango, wanda da farko yake goyon bayan ‘dan takarar jam’iyyar NNPP, Rabi’u Kwankwaso, daga bisani ya sauya sheke zuwa sansanin Tinubi yayin zagayen APC a gidan wasan Sani Abacha a Kano.

Tsohon gwamnan jihar Legas, a ranar Talata da Laraba, ya tattara dumbin magoya baya daga jihohi bakwai na yankin Arewa-maso-yamma a tarin ayyukan kamfen dinsa. Tinubu yayi alkawarin dawo da masana’antun da suka mutu a kasar tare da taimakawa wajen magance matsalar gararambar yara a matsayin almajirai idan aka zabesa a matsayin shugaban kasa a zaben watan Fabrairu.

“Ba muyi mamakin ganin irin tarin mutanen da suka hallarci kamfen din ba, saboda hakan na da nasaba da cigaban da gwamna Abdullahi Ganduje ya kawo. Haka zalika, irin wannan cigaban ne Tinubu ya samar a Legas yayin da yayi gwamnan Legas. “Tinubu ne ya taimaka wajen cigaban Legas ba tare da duba da addinin kowa ba. Wannan shi ne dalilin da yasa muke kira gareku da ku fito ku saka masa kuri’u da Nasir Gawuna da dukkan ‘yan takarar APC na Kano.” – Cewar Ali Nuhu.

Sauran jaruman da suka halarci wurin gami da marawa Tinubu baya sun hada da darakta kuma jarumi Falalu Dorayi; jarumi kuma S.A din Ganduje Mustapha Naburaska; jarumin barkwanci Suleiman Bosho; Jarumin barkwanci Baba Ari; jarumin barkwaci Dangwari; da sauransu.

Labarai Makamanta