Jaruman Kannywood Sun Nesanta Kansu Da Fim Din Badala


A daidai lokacin da labarin fim din Makaranta ya ke ci gaba da yamutsa hazo tare da yin tofin Allah tsine ga masu shirya fim din, sai ga shi Shugaban kungiyar Jaruman kannywwod Alhassan Kwalle ya fito ya nesanta kungiyar su da wannan fim din.

A tattaunawar da Jaridar Dimukaradiyya ta yi da shi ya bayyana cewar.

“Mu a matsayin mu na kungiyar Jarumai ba mu da wata Alaka da wannan fim din mai dogon zango da aka fara tallan sa a kafafen sada zumunta domin ba Yan kungiyar mu ne suka shirya shi ba, don haka mu ba mu da wata alaka da shi.

Sannan kuma muna yin Allah wadai da masu shirya shi domin kuwa fim ne da zai bata tarbiyyar jama’a saboda haka muke Kira ga hukuma, lallai ta yi gaggawar daukar mataki a Kan masu shirya fim din saboda illar da zai haifar a cikin jama’a.”

Daga karshe ya yaba wa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano saboda matakin da ta dauka na neman masu shirya fim din domin a hukunta su.

Labarai Makamanta