Janye Tallafin Mai: Za Mu Tsunduma Yajin Aiki Mafi Muni A Tarihi – Kungiyar Kwadago


Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar bayan gaza cimma matsaya tsakanin ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya da kuma gwamnatin tarayya game da batun janye tallafin man fetur, ga dukkan alamu babbar ƙungiyar ma’aikata ta ƙasar NLC na kan ƙudurinta na shiga yajin aiki daga wannan mako.

Bayanai dai sun ce ƙungiyar ta NLC ta ƙauracewa taron da gwamnatin ƙasar ta kira a ranar Lahadi, inda rahotanni suka ambato ƙungiyar tana cewa ba za ta yi wata tattauna da wakilan gwamnati ba, har sai an kafa halattaccen kwamiti.

Sai dai takwararta ƙungiyar TUC ta halarci taron, inda ta buƙaci gwamnati ta koma kan tsohon farashin man fetur kuma ta ƙara mafi ƙarancin albashi da ma’aikata ke karɓa a Najeriya.

A ranar Lahadi ne gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta sake kiran taro da ƙungiyoyin ƙwadagon a ci gaba da tattaunawa don hana su shiga yajin aikin da suka ƙuduri aniyar tafiya daga ranar Laraba mai zuwa.

Sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da Kwamared Nasir Kabir, sakataren tsare-tsare na haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago ta NLC, ya ce babu buƙatar ci gaba da tattaunawa da gwamnati.

“Babu abin da gwamnatin tarayya ta yi a kan sharuɗɗan da muka bayar cewa a janye batun cire tallafin mai, don haka tun da gwamnati ta ƙi daukar mataki mu kam a ɓangarenmu ba gudu ba ja da baya.

Za mu tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya baki daya” in ji Kwamared Nasir.

Kwamared Nasir Kabir, ya ce “Mun bayar da sharuda kamar na gyara matatun mai ta yadda za a rika samar da mai daga wajensu a kasa, sannan kuma shi kansa tallafin ba a cire shi sai an kawo abin da zai saukakawa mutane hali da za su iya shiga bayan janye shi”.

Ya ce, basu ji dadi ba saboda gwamnatin Najeriya ta dauki matakin janye tallafin mai ba tare da kawo abubuwan da za su saukaka wa ‘yan kasar radadin janye tallafin man ba.

Sakataren tsare tsare na hadaddiyar kungiyar kwadagon ta NLC, ya ce batun cewa nan gaba za a ga alfanun janye tallafin mai a Najeriya, duk zance ne kawai.

“A baya ma anyi haka amma ba abin da aka gani, don haka ko shakka babu a yanzu ma babu wani alfanu da za a gani illa jefa ‘yan Najeriya a cikin mawuyacin hali” in ji shi.

Ya kara da cewa “bisa la’akari da haka mun ba wa gwamnati wa’adi matukar bata dawo da tallafin mai ba, to a ranar Laraba bakwai ga watan Yunin 2023, zamu shiga yaji aiki”.

Kwamared Nasir Kabir, ya ce za su yi wannan yajin aiki ne don nuna fushinsu a kan karin farashin mai da aka yi, wanda kuma duk wani mai kishin Najeriya zai goya musu baya.

A cewarsa, “kowa ya san ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali, sannan kuma azo a kara musu wata ukubar, wannan sam ba daidai bane”.

Tun bayan sanarwar da shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya yi a ranar da aka rantsar da shi ta cire tallafin man fetur, aka samu karin farashi da kuma fara dogayen layukan mai a sassan kasar.

Hakan ne ya sa kungiyar NLC din ta ce ba za ta amince da wannan halin ba, saboda janye tallafin zai jefa al’umma cikin wahala.

Labarai Makamanta

Leave a Reply