Janye Tallafin Mai Shi Ne Mafita A Najeriya – El-Rufa’i

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi hasashen manyan matsalolin da sabon shugaban Najeriya zai fuskanta inda ya kama aiki, El-Rufai ya ce dole ne wanda zai karbi mulkin kasar nan ya yi kokarin shawo kan matsalar tattalin arziki.

Gwamna Nasir El-Rufai ya ce don haka akwai bukatar a magance matsalar tallafin man fetur da kuma tashin da kudin kasar waje suke yi a halin yanzu.

Gwamnan na Kaduna ya ce idan shugaban kasar da aka zaba ya yi wadannan abubuwa, zai yi masa wahala ya zarce kan mulki a 2027.

El-Rufai ya yi wannan jawabi a wajen wata tattaunawa da bankin Duniya ya shirya a garin Abuja a kan abin da ya shafi cigaban tattalin arzikin Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da aka yi masa tambaya a kan cire tallafin man fetur, tsohon Ministan birnin Abuja yana cewa dole a kawo karshen tsarin nan domin shine kadai hanyar da ta rage na fita daga matsalar da ake ciki a harkar mai.

A cewar Gwamnan, a baya Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yarda za a janye tallafin a shekar nan, amma aka fasa sai zuwa tsakiyar shekarar 2023. Kamar yadda El-Rufai ya fada a taron, Gwamnatocin jihohi da ‘yan kasuwa sun yarda cewa babu yadda aka iya, wajibi ne a hakura a daina biyan tallafin mai.

Labarai Makamanta