Jangeɓe: Maigadin Makaranta Na Cikin ‘Yan Bindiga – Matawalle

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce ‘yammatan Makarantar Jangebe sun bayyana cewa maigadinsu na makaranta yana daga cikin wadanda aka hada kai dasu aka sacesu.

A ranar Laraba da ta gabata ne Matawalle ya bayyana hakan a shirin siyasarmu a yau na gidan Talabijin na Channels.

A yayin da aka bukaci ya bayyana wadanda suka sace yaran, gwamnan yace ‘yan bindigan sun sanar da cewa har da maigadin suka hada baki. Matawalle yace ana bincike a kan haka amma bai sanar da sauran wadanda aka hada kai dasu ba.

“Har da maigadin makarantar. Yaran sun sanar da hakan kuma sun ce bayan an sakesu, ‘yan bindigan sun ce su gaishe musu da maigadin makarantarsu,”.

“Sun kara da bayyana sunansa a matsayin wanda ya ce su zo a lokacin su kwashe yaran, don haka da hannunsa a ciki. “Sun sanar da hakan a gaban kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, za a yi bincike a kan hakan sannan a gano dukkan wadanda ke da hannu a ciki.”

Kimanin dalibai mata 270 ne ‘yan bindigar suka sace a harin da suka kai makarantar tasu dake Jangeɓe ƙaramar Hukumar Talatar Mafara ta jihar Zamfara, kafin su kubuta daga baya, bayan sun shafe tsawon kwanaki a hannun su.

Labarai Makamanta